Assalamu alaikum. Mal. Adams naga duk bayananka. Ina nan kuma ina lekowa hi5, ba dai ma haduwa ne domin na dade ban shiga Hausa World Connection ba. Game da labarin mutumin nan mai mata 86 (ba 78 ba), ai ni na fara kai labarinshi waccan majalisar, in ka bincika sakonnin zaka gani. Ina kuma sane da martanin da ka rubuta game da tofin Allah tsine da na taba cewa a yiwa Geert Wilders dan kasar Holland a ita dai majalisar. Na gode, ka huta lafiya.